Headlines
Loading...
Yadda Zaki Hada Sabaya Domin Kibar jiki

Yadda Zaki Hada Sabaya Domin Kibar jiki



Sabaya wani ingantacce hadine da kasashen larabawa ke  amfani dashi ga mace dake da ciki ko mai shayarwa ko maza dake bukatar jikinsu yayi kyau sosai. 


Ana amfani dashi a kasashe daban-daan a fadin duniya, yankin larabawa wannan ba bakon abu bane 


Ana hada sabaya ingredients, domin amfanin mata masu aure da mara aure, da ma maza masu son jikin su.


Sabaya nada matukar amfani a jikin mata, wajen gyaran nono, da sauran su


Amfanin sabaya ga mata da maza


1. Gyara nono 

2. Gyara fata 

3. Lafiya jarirai

4. Ciko da mai rama

5. Dauke rama gamai azumi

6. Samar da ingantacciyar lafiya na gaban maza

7. Samar da lafiyayyan maniyyi 

8. Samar ga niima ga duk macen dake da karancin niima. 



Kayan hada SABAYA


1. Ridi gwangwani 2

2. Hulba original gwangwani 2

3. Gyada gwangwani 2

4. Waken suya rabin Kwano 

5. Shinkafa rabin Kwano 

6. Alkama rabin Kwano 


Yadda ake hadin sabaya


Za'a soya gyada da ridi.


Sannan a jika shinkafa da alkama tsawon awa biyar 5, sai a cire su a shanya.


Sai a hada su waje guda dukkansu a nika


Yadda ake dama kunu zaa dinga damawa da madara da zuma cokali 3 duk mutum 1


Duk Wanda ke jin wahalar azumi don Allah ya fara shan wannan daga lokacin yagama jin azumi zai dumul dumul fatar shi zata dinga sheki.


Matar da nononta ya fadi ina da yakini idn ta fara shan SABAYA zai dawo Kamar na budurwa.



Haka ana ba yara da macen dake shayarwa ko mai ciki zatai mamaki yadda zata haifi lafiyayyen yaro.


Haka macen dake shayarwa nononta bazai taba faduwa ba ko tayi rama in dai tana shan SABAYA da izinin Allah. 


RAMA (UNDERWEIGHT)


Rama dai alama ce dake nuna cewa ma'aunin jikin mutum bai kai 18.5 ba. Galibi abinda ke kai mutum ga wannan halin yana da alaqa ne da qarancin Vitamins a ciki ko Minerals sai bushewar fata, ko iske garkuwar jikin mutum ta gaza yaqar cututtukan dake addabar jikin. 


Sai qarancin jini ko ya kasance qiyasinsa ya yi qasa, ko kuma tun asali jikin ya gaza wurin tsakuro abinda yake buqata daga abinda mutum yake ci, masamman in ya kasance ba abinda yake so ne mutum yake ci din ba, wannan yana haifar da raunin qashi, ko ramar jiki.


Hadin SABAYA yana da matukar tasiri sosai wajen gyara jiki, yayi kyau yayi mulmul.

0 Comments: