Maganin sanyi iri-iri na Maza da Mata daga Juwairiyya
Mahimman bayanai
- Fiye da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i (STIs) miliyan 1 ana samun su kowace rana a duk faɗin duniya, yawancin su basu bayyanar da wata alama ga jikin dan adam.
- A kowace shekara ana samun sabbin cututtuka miliyan 374, tare da 1 daga cikin 4 na STIs masu warkewa ne: chlamydia, gonorrhea, syphilis da trichomoniasis.
- Fiye da mutane miliyan 500 masu shekaru 15-49 an kiyasta suna kamuwa da cutar ta al'aura sanadiyyar kwayar cutar herpes simplex (HSV ko herpes).
- Kwayar cutar papillomavirus (HPV) tana da alaka da mace-mace sanadiyar cutar kansar mahaifa sama da 311 000 kowace shekara.
- Kusan mata masu juna biyu miliyan 1 an kiyasta sun kamu da cutar syphilis a shekarar 2016, wanda ya haifar da sakamakon haihuwa mara kyau kusan 350 000.
- Cutukan sanyi (STIs) suna da tasiri kai tsaye akan lafiyar jima'i da haihuwa ta hanyar kyamar juna, rashin haihuwa, ciwon daji da matsalolin ciki kuma suna iya kara hadarin kamuwa da HIV.
- Sanadiyar yawan shan magunguna mara inganci barkatai, mutane na fuskantar babbar barazana magance cutukan sanyi (STIs) a duk duniya.
Dubawa
Fiye da kwayoyin cutar sanyi talatin 30 na Bacteria, Viruses da parasite an san ana yada sune ta hanyar jima'i, ciki har da jima'i na farji, dubura da na baki.
Wasu cutukan sanyin (STIs) kuma ana iya yada su daga uwa zuwa yaron ta a lokacin da take da ciki, ko haihuwa da shayarwa.
Kwayoyin cuta guda takwas suna da alaka mafi girma da jima'i. Daga cikin wadannan, cutar sanyi 4 a halin yanzu ana iya warkewa daga gare su, sune: syphilis, gonorrhea, chlamydia da trichomoniasis.
Sauran hudun 4 kuma cututtukan sanyin da ba za a iya warkewa ba ne, sune: Hepatitis B, Herpes simplex Virus (HSV), HIV da Human papillomavirus (HPV).
Mai karatu barka da zuwa shafin uwar gulma. A yau kuma zamu kitso maku ilmi akan ciwon sanyi da maganin ciwon sanyi mai inganci.
Bayan dan karamin bayani a sama wanda mukayi domin ku samu karin fahimta. Zamu ci gaba da bayanin mu mai dauke da fa'ida dangane da maganin sanyi (infection), maganin sanyi kowane iri na musulunci, na gargajiya da na bature.
Wannan bayani ya da da maganin sanyin maza da mata sanyin gaba mai takurawa yayin jima'i.u
Bayan samun karanta wannan bayani namu, mai karatu zai samu cikakken fahimtar maganin sanyi, da yadda ake hada maganin da kuma yadda ake amfani da maganin sanyin. Bari mu ci gaba da bayani.
Menene cutuar sanyi ko ciwon sanyi?
Ciwon sanyi infection (STI), ciwo ne da ake kamuwa da shi ta hanyar jima'i ko sanadiyar kazanta da yake bayyana alamomin wasu sabon fitar ruwa daga al’aura, azzakari ko farji· jin zafi lokacin fitsari ko yayin jima'i, kuraje, da kyakyawin gaba.
Duk wadannan alamomi, yana da matukar muhimmanci ku sani akwai lokutan da zaku iya kamuwa da ciwon sanyi batare da jin wasu alamomi ga jiki ba.
Jin alamomin ciwon sanyi ya danganta da kalar cutar, girman ta, da dadewar ta a cikin jikin dan Adam (mace ko namiji).
Bari mu ga bayani akan kashe-kashen wadannan cutaka domin sanin su da iya magance su.
Kashe-kashen Cutar sanyi.
Cutar Human papillomavirus kamuwa
Mutane da yawa masu fama da HPV ba sa jin wata alama amma har yanzu suna iya cutar da wasu ta hanyar jima'i. Alamun na iya haduwa da cutar warts a al'aurar ko fatar da ke kewaye da ita.
Cutar Herpes na al'aura
Ciwo, kaikayi da kananan raunuka suna bayyana da farko. Suna haifar da ulcers da kuraje masu tauri. Bayan kamuwa da cutar a karon farko, cutar herpes na al'aura na kwance cikin jiki, sai daga baya alamun ta ya dawo kamar bayan shekaru.
Cutar Chlamydia
Yawancin wadanda ke dauke da cutar chlamydia ba sa bayyanar da alamomin ta, amma ku sani suna iya cutar da wasu ta hanyar jima'i. Alamun ta kuma na iya hada da ciwon al'aura da fitar ruwa daga farji ko azzakari.
Cutar Gonorrhea
Alamomin sun hada da fitsari mai radadi da fitar ruwa daga azzakari ko farji. Maza na iya samun ciwon yayan maraina su kuma mata na iya jin zafi a kasan cikin su saman mara. A wasu lokuta, cutar gonorrhea ba ta bayyanar da alamomi.
Cutar Kanjamau (HIV/AIDS)
Wasu masu dauke da kwayar cutar kanjamau suna samun alamun mura kamar makonni 2 zuwa 4 bayan kamuwa da cutar.
Mutanen da ke shan magungunan HIV kila ba za su sami wasu alamun cutar ba tsawon shekaru.
Yayin da kwayar cutar ke karuwa kuma tana lalata kwayoyin halittar garkuwar jikin dan adam, alamun cututtuka na iya tasowa kamar zazzabi, gajiya, da kumburin a wasu sassan jiki. Idan HIV yaci gaba ba tare da magani ba, yakan juya zuwa AIDS a cikin kimanin shekaru 8 zuwa 10.
Cutar syphilis
Matakin farko ya kunshi kumburi mara zafi akan al'aura, dubura ko baki. Bayan ciwon farko ya warke, mataki na biyu yana da bayyanar da kuraje. Bayan haka, alamun sa zasu washe har sai mataki na karshe wanda zai iya faruwa bayan shekaru. Wannan mataki na karshe zai iya haifar da lalacewar kwakwalwa, jijiyoyi, idanu ko zuciya.
Wadannan cutukan sanyin duka ana kamuwa dasu ta hanyar jima'i, da sauran hanyoyi kuma.
Zamu ci gaba da maganar cutukan sanyin da ke addabar maza da mata dake kawo masu cikas a cikin rayuwar subta aure. Sannan mu kawo hanyoyin magance su cikin sauki.
Alamomin ciwon sanyi
- Fitar farin ruwa.
- Sanyi mai rike gabobi
- Jin zafi yayin saduwa
- Mura/Tari/Majinar kirji
- kankancewar mazakuta
- Ciwon mara lokacin al’ada
- Rashin kuzari lokacin jima’i
- Karancin maniyyi
- Karancin sha’awa
- Mataccen Maniyyi
- Tsinkewar maniyyi
- Kumburin maraina
- Kaikayin matse matsi
- Warin gaba
- Fitsarin jini
- Zafin fitsari
- Ciwon Mara
- Sanyin kashi
- Kurajen gaba
- Amosanin Mara
Yadda ake gane ciwon sanyi.
Alamomi suna bayyana ga wanda yake da ciwon sanyi. Sannan ana fahimtar mutun yana da cutar idan wadannan alamomin sun bayyana.
Awon Asibiti
Aune-aunen jini, fitsari ko ruwan jiki a sashen awo na asibiti yana daya daga cikin abinda ya ake yi domin gane ciwo sanyi.
Ana gane ciwon sanyi na gonorrhea, syphilis, HIV, Herpes da sauran su ta hanyar awon jini, fitsari, ko ruwan jiki mara lafiya.
Gwajin Tantancewa (Screening)
Gwajin STD ko kamuwa da cutar ta hanyar jima'i a cikin wanda ba shi da alamun cutar ana kiransa gwajin tantancewa. Yawancin lokaci, gwajin STI ba gwaji ne na yau da kullun ba a shashen lafiya. Sai dai yana da matukar amfani ace kowa ne mutun yayi shi.
Kwararru a sashen lafiya, suna matukar bayar da shawara ga al'umma akan suyi gwajin tantancewa (screening) a asibiti.
Gwajin tantancewa ga masu sabon aure.
Yana da kya masu son yin aure suyi gwajin HIV, Hepatitis B da saura gwaje-gwaje kafin suyi aure.
Gwajin tantancewa na HIV ga kowa
Masana harkar lafiya, suna bayar da shawara kowa ne daga dan 15 zuwa 65 ya kasance yasan matsayin sa dangane da cutuka. Kamar AIDS da kwayar cutar HIV ke kawowa ta hanyar awon jini ko yawun mutun a asibi.
Mata masu juna biyu
Yana da kyau mata masu juna biyu suyi gwajin tantancewa, domin kowace mace mai ciki ana iya mata gwajin HIV, hepatitis B, chlamydia and syphilis a lokacin da take da juna biyun. Wasu masana sun kara da gwajin cutar gonorrhea da hepatitis C ga kowace mai juna biyun.
Maganin ciwon sanyi.
Ana iya magance STDs ta hanyoyi daban-daban dangane da musabbabin ciwon.
Cututtukan da kwayoyin cutar bacteria ke haddasarwa ta hanyar jima'i suna da matukar saukin magancewa.
Ana iya magance cututtukan STI da kwayoyin cutar virus ke haifarwa amma ba koyaushe ake warkewa ba.
Idan kina da ciki kuma kina da cutar sanyi (STD), samun maganin sanyi da wuri zai iya hana ko ya rage hadarin kamuwa da jaririn dake ciki.
Maganin sanyi da ake dauka ta hanyar jima'i yawanci ana magance shi ta hanyoyi daban-daban.
Maganin sanyi na hausa
Hausawa suna magani da furanni, yayan itace, sayyun itace, ganye da sassake, da sauran abubuwa domin magance cutar sanyi.
Idan mace ko namiji yana dauke da cutar sanyi ga abubuwan da zai samu ya hada domin magance shi.
Da farko dai za ki ko ka samu ganyen gwanda ki ko ka wanke da masu dumi da gishiri, amma ba wai dirjewa ake yi ba sama-sama za a wanke saboda dattin da ke jikin ganyen da sauran cututtuka su fita.
Sai ki ka ka samo tsamiya, citta, tafarnuwa da gishiri. Ki ko ka samu ruwa sai ka ko ki zuba kamar lita goma 10, kad a wuce goma din.
Sai ka ko ki saka ganyen gwanda, tsamiyya, citta, da tafarnuwar a ciki sannan ki zuba gishiri babban cokali biyu 2, a dora a wuta a tafasa shi sosai da sosai.
Yanda za a sha maganin sanyi.
Za a dinga shan ruwan safe da dare in sha Allah duk wani abu da ya danganci ciwon Sanyin mata da maza za'a samu warkewa.
Maganin sanyi na bature.
Akwai kalolin maganin sanyi na bature, kamar yadda zamu kawo maku su da bayanan su kamar haka:
Magungunan Antibiotics.
Sau da yawa idan mutum ya fara shan maganin antibiotic na iya warkar da yawancin ciwon sanyi (STIs) da wasu kwayoyin cuta ko kwayoyin cuta ke haifar da cutar sanyi, kamar gonorrhea, syphilis, chlamydia da trichomoniasis.
Da zarar ka fara maganin sanyi na antibiotics, ana bukatar a kammala su duka kamar yadda likita ya rubuto.
Magungunan Sanyi na Virus.
Idan kana da cutar sanyi da kwaya vutar virus ta kawo ko kuma kanjamau HIV, likitanka na iya rubuta maganin da ke hana kara tsananin cutar ta hanyar sha maganin sanyi na virus.
0 Comments: