Headlines
Loading...
Cikakken Tarihin fatima hussain labarina 2024

Cikakken Tarihin fatima hussain labarina 2024



Tarihin fatima hussain labarina, baya kammaluwa face an sanya gwarzon ta, jigon ta wanda ya haskaka ta wato malan Aminu saira. Malan Aminu saira shine mamallaki kuma mai bada umarnin shirin nan mai dogon zango wato labarina. Kuma shine ya mata rada mata suna "Maryam", wadda daukacin al'ummar kasar Najeriya kamar mutanen Kano, Kaduna, Sokoto, da Abuja suka fi sanin ta da suna Maryam labarina.



Asalin ta tarihin fatima Hussain labarina



Sunan ta na asali shine Fatima Hussain, an haife ta a January 3, 1998, jahar Kaduna arewacin Najeriya, a karamar hukumar makarfi Kaduna. 


A wata majiya mai inganci, anjiyo cewa asalin mahaifan Fatima hussain daga jahar Borno suke, inda sukayo hijira zuwa jahar Kaduna duk a arewacin Najeriyar.


Karatun fatima hussain a Kaduna



Fatima Hussain labarina, tayi karatun ta na farko (primary school education) a Betty Queen International Primary School daga shekarar 2004 zuwa 2010. Bata tsayanan ba inda ta cigaba da karatun ta zuwa makarantar sakadare wato (secondary school education) a Government Secondary School Birnin Yero, kuma ta samu nasarar kammalawa daga shekarar 2011 zuwa 2017.


Fatima Hussain labarina na da burin ta koma babbar makaranta bayan kammala sakandare, domin samun ilmi na gaba wato degree a jami'a. 


Karatun ta na Babbar Makaranta a Kaduna


Burin karatun fatima a jami'a bai cika ba, saboda haka sai ta cigaba da karatu a makarantar fasaha ta Kaduna, wato Kaduna polytechnic inda ta kammala karatunta a 2021. 


Fatima Hussain ta samu takardar diploma a fannin kimiyar aune-aune da gwajin jinin bil'adama wato Science Laboratory Technology (SLT) a makarantar Polytechnic ta Kaduna, Najeriya.


Zaman ta tauraruwa a shirin labarina



Shirin mai dogon Zango "Labarina" da ake hasakwa a tashar talabijin ta Arewa24 na Malan Aminu saira, Saira movies Kano. Shine shirin farko da Fatima Hussain ta fara bayyana a masana'antar ta Kannywood daga shekarar 2023 zuwa yau. 


A wannan shirin fatima tayi matukar fice, wanda yasa ta samu dumbin masoya a yankunan arewacin Najeriya musamman a jahar Kano da Kaduna.



Amma hakikanin gaskiya Fatima ta samu masoya a duk fadin kasar ta Najeriya dama wasu sassan Afrika ta yamma.



Fatima Hussain tauraruwa ce mai haskawa a wannan lokacin, kuma tayiwa sauran taurarin masana'antar shirin hausa ta Kannywood fice a wannan karnin.



Daga bakin masoyan fatima Hussain


Munyi tsammanin sunan ta 'Maryam" ne, inji masoyan fatimar, kuma muna son Fatima ne saboda tsantsar amanar ta da hakuri da kuma kawaici ga abin duniya.



Tabbas masana sunce asalinta bata da bukatar rayuwar kyale-kyalin duniya. Ita dai tafi maida hankali ga abinda ta mallaka ba hangen na wani ba.



Shin wannan dabi'ar na daya daga shilar farin jinin ta?



Har yanzu ana cikin cece-kuce akan wanga irin farin jini na fatima hussain, a tarihin jaruman kannywood anyi ittifaki babu wani jarumi ko jaruma da a karon farko nan take ta samu irin wannan karbuwa ta fatima ga al'umma. 


shafin mu na uwar gulma ya zage damtse domin sabun ta maku tarihin maryam hussain labarina, a duk lokacin d muka samu wani karim bayani. Kamar masu neman fatima hussain

 labarina phone number, ko masu son hira ko auren ta duka wata rana zamu sada ku da ita domin kuji ta bakin ta.


Uwar gulma ji da kunnen ku.


0 Comments: