Maganin kaikayin gaba
Kina fama da yawan kaikayin al'aura ko zuban farin ruwa mai wari, ko kurajen gaba, ko tsananin bushewa, Ko mijinki yana fama da matsaloli bayan saduwa dake, to ga magani in sha Allahu.
- ZUMA (A AJIYE A GEFE)
- LEMON TSAMI : MANYA GUDA UKU KO HUDU.
- CITTA MAI YATSU - 4 (MANYA)
- GANYEN MAJAMFARI (RABIN KOFI).
- NAMIJIN GORO - GUDA BAKWAI.
- TAFARNUWA - MANYA GUDA 3.
Ki nika namijin goron tare da cittar. Sauran kuma ki kirbasu a turmi ko a blender. Sannan ki zuba ruwa kofi bakwai a tukunyarki ki zuba dukkan kayan hadin acikkn sannan ki tafasasu akan wuta.
Bayan ya huce sai ki rika shan kofi guda (karamin kofi) safe da yamma tare da zuma cokali uku ko hudu zaki zuba acikin kofin, ko kuma yadda zai isa.
Zaki ci gaba da sha har tsawon kwanaki goma zuwa sati biyu. Maza da Mata duk zasu iya sha domin magance Gonorrea ko ciwon sanyi mai sanya fitar farin ruwa ko melewar fatar al'aura ko kaikayi ko fitar kuraje, musamman irin wanda ake dauka yayin jima'i.
Alokacin da ake amfani da wannan hadin, ana so mace ta samo Jan Algarur (Habbur Rashad) mai kyau. Ta rika dafawa (cokali 2 ko 3) tana surkawa daidai gwargwado sannan ta shiga ciki ta zauna ta dumama gabanta tsawon minti goma. Kullum zatayi sau 1.
Shi kuma Namiji zai rika shan H/rashad din acikiin kunu ko madara ko nono, rabin karin cokali kullum har tsawon sati biyu.
Wannan fa'idar kyauta ce (Goron Sallah) daga ZAUREN FIQHU zuwa ga dukkan al'ummar Musulmai maza da mata musamman masu bibiyar shafukanmu na internet. Kuma anyi izinin turashi zuwa ga groups na whatsapp da facebook amma aji tsoron Allah kada a chanza koda harafi guda acikin rubutun nan.
DAGA ZAUREN FIQHU
Post a Comment
0Comments