YADDA CUTAR BAN DAKI TAKE GUSAR DA
NI'IMAR MACE
Na shigo ne a yau don yin nazari tare da tunatar
da ku matsalolin da ake samu a ban daki na
kwayoyin cututtuka. Ina masu fama da kwayoyin
cuta da ake samu a yayin zaman biyan bukata a
ban daki? Dalilin yin magana a kan wannan cutar
don kusan jama’a da dama suna fama da ‘Toilet
Infection’ a Turance.
Ya kamata uwargida ta fahimci cewa kwayoyin
cutar da ake samu a ban daki suna da hatsari
matuka ga ‘ya mace. Na farko suna hana
haihuwa, kwayoyin cutar suna saurin busar da
duk ni’imar mace. Wannan ya sa duk kwaliyyar da
kike yi, bata lokaci ne, maigida ba ze gani ba,
saboda ya san idan ya kusance ki lokacin
(SADUWA DAKE) , ba ki da wani dandano a tare
da ke. Irin haka ke haifar da matsaloli a tsakanin
ma’aurata, don ba abin mamaki ba ne uwargida
ta yi tunanin maigida ya tsane ta ne, alhali babu
wata tsana, ke ce dai ba ki kulawa da kanki
yadda ya kamata.
Yana da kyau uwargida ta dauki wannan da
mahimmanci wajen gano bakin zaren, kana ta yi
tsayin daka don magance cutar baki dayanta.
Shin me ya kamata ki yi don magance cutukan da
ake kamuwa da su ban daki? Ki tanadi wadannan
ayayyakin kamar haka:
(1) Lalle da ganyen magarya, ki rika shiga ciki
kina zama
(2) Bayan nan kuma, ki samu man Zaitun, man
Tafarnuwa, man Hulbah, ki hada su da miski, sai
a rika turawa a gindin ki Wannan babban sinadari
ne matuka yana inganta mace ta kasance mace
mai amsa sunanta, sannan ya warkar da
cututtukan.
(3) Za ki iya samun bagaruwa da ganyen
magarya , garin Hulbah, garin Habbatus-sauda, ki
hada su wuri daya, ki tafasa su sosai , idan kika
sauke, ki bar shi ya huce amma da duminsa ki
rika zama a ciki.
(4) Ki samu man Tafarnuwa, man Hulba, man
Habbah, ki dinga sha a kai- a kai, shi kuma zai
kashe miki cututtukan da ke cikinki.
(5) Amfani da miski musanman bayan gama
al’ada yana matukar taimakawa, sannan kuma
yana dawo miki da ni’imar da kika rasa lokacin
da kike al’ada.
(6) Za ki samu saiwar Zogale da Tafarnuwa ki
dafa su a tare, idan kika sauke, ki bar shi ya
huce, sai ki zauna a ciki da dan duminsa, har sai
ya huce gaba daya za ki fita.
Bayan duk wadannan, ya ke uwarigda da sauran
aiki, domin ana son ki dinga amfani da ruwan
dumi mussanman lokacin da kike al’ada.
Amma mafi mahimmanci a rika tsaftace ban daki
a koda yaushe, don rashin tsaftace shi zai iya
haifar da cututtukan da ba za a iya sanin
hakikansu ba. Kana kuna mutum ya kasance mai
wanke hannayensa a duk lokacin da ya fito daga
ban daki da sabulu ba ruwa kawai ba.
Da fatan za ku yi amfani da wannan damar wajen
inganta rayuwarmu, tun kafin cututtuka su ci
galabanku.
Haka kuma bayan amfani da albasa don maganin
rashin dandano da rigakafin wasu cututtuka, har
ila yau ta yarda da amfani da albasa wajen
maganin sanyi da tari asma da ciwon sanyi
(bronchitis).
Albasa kan rage maikon dake cikin jini. A kasar
Indiya a wasu wuraren da basa yin amfani da
albasa akan same su da maikon cikin jini da
cushe jijiyoyin dake tafiyar da jini akan wadanda
suke amfani da tafarnuwa da kuma albasa.
Albasa na bada kariya wajen kara kumburi game
cutar daji.
Har ila yau albasa na bada kariya wajen ciwon
ciki, da cutar daji da sauran cututtuka. Tana
karawa huhu karfi musamman ga masu cutar
asma.
A wani bangaren kuma, yana da kyau a lura da
cewa, idan an yanka albasa rabi, to kodai a sa a
cikin firinji ko a yar da sauran don kuwa idan aka
bar ta ta kwana a yanke, in har an yi amfani da
ita za ta cutar da mutum don ita albassa ta
kasance kamar kura ce ga ‘kwayoyin
cuta
0 Comments: