Headlines
Loading...
Kishi kumallon mata: Saura Kadan Aurenta Ya Mutu

Kishi kumallon mata: Saura Kadan Aurenta Ya Mutu

Kishi kumallon mata: Saura Kadan Aurenta Ya Mutu.



Na kwana ina sake-sake a raina tun lokacin da Isah mijina ya ce da ni da sassafe zai tafi Kano, ya kasa fada min takamaiman dalilin da zai kai shi Kano ba, alhali ba hutu ya dauka a wajen aiki ba. Na ji a raina sam ban yarda da shi ba, da gangan na ki tashinsa amma tun kafin a kira assalatu na ga ya tashi ya fara shiri sai na sake gasgata zargina na tabbatar lallai tafiyar nan ta sa ta na da nasaba ta wani muhimmin abu da yake boye min


Tun gari bai gama wayewa ba ya dawo daga masallaci ya dauki jaka ya ce min zai tafi. Ban kula shi ba, kudin cefanen ma a akan mudubi ya ajiye ya tafi abinsa. 


Daman gidanmu akan bene yake kuma a akan babban titin hanyar kano, Ina tsaye a jikin windo ina lekensa hannun dama ya kamata ya bi in dai kano zai je sai na ga ya yi hanyar hagu cikin gari kenan, daga nan na tabbatar ba kano zai tafi ba wata sharholiyarsa kawai zai tafi. 


Zuciyata ta hau tafarfasa, ban iya tashin yara na yi musu wanka don zuwa makaranta ba, na yi wuf na fito kofar gida. Daga ni sai zani daurin kirji sai kuma hijabi da na saka. Ina ta kai kawo a tsakiyar titi na rasa yadda zan yi in bi bayansa, na so in tari acaba sai dai kash! na san ya yi min nisa ba zan san in da ya bi ba. Makwabta sun gaji da tambaya ta ko lafiya suka ganni a cikin wannan yanayi? A tunaninsu ko wani tashin hankali ne ya faru da yarana ko mai gidana nake neman agaji. Ko amsa ban iya basu ba har suka gaji suka bar ni.



Ina cikin wannan hali sai kwatsam na hango motar Isah ya zo zai wuce, gaban motar kuwa wata zukekiyar budurwa ya dauko ko gyale bata saka ba, bayan motar kuwa ‘yan mata ne guda uku kawayenta kenan, dan haka na tabbatar zargina ya zama gaskiya. Na falfala da gudu tsakiyar kwalta na sha gaban motarsa, sai dakyar ya iya taka burki ya tsaya, saura kadan ya buge ni. 


Na tafi a guje na bude gaban mota na kasuma muka zauna tare da wannan budurwa, tana harara ta ina hararar ta. Isah bai ce min komai ba, ya kasa hada ido da ni, nima ban ce masa komai ba na san dai yau ko ana haa-maza-haa-mata sai na ga in da zai kai su don ba zan fita daga motar ba. Ya ja mota muka fara tafiya. Wasa-wasa tafiya ta mike har muka fita daga cikin garin Jos muka kama hanyar Kano. Ba mu tsaya a ko ina ba sai a wani gari da ake kira shima wata ce daga bayan mota ta ce “direba, in ka karaso wudil zan sauka, ya tsaya a wudil ta miko masa kudin mota ya bata canji.



Sai na ji jikina ya yi sanyi ashe fasinjoji ne, na rasa abinda yake yi min dadi. Da aka yi gaba ma guda biyu suka ce zasu sauka ta gaba da daya a baya. Aka tsaya a ka sauke su su ka bashi kudin motarsa. Sai ni kadai na rage a gaba da wata a baya itama muna shiga Kano ta ce a sauke ta, aka sauke ta. Daga ni sai shi, sai a lokacin ya dube ni cike da takaici ya ce, “ke kuma a ina za ki sauka tunda mun zo kano?”



Na yi shiru na kasa hada ido da shi daga nan na shiga bashi hakuri. Ya girgiza kai ya ce, “ai ni da ke zamanmu ya kare daga yau, kin zo a dai-dai sai ki wuce gidanku daga nan. Wa kika barwa yarana?”



Sai a lokacin na tuna na bar yarana guda uku kanana, babban ne ma yake da shekaru shida, karamin shekaru hudu, sai mai shan nono shekara daya, na bar gidan bude babu babba. Na dora hannu aka fasa kuka, ina mai magiya ina bashi hakuri. Ransa ya baci sosai, a take ya tsayar da motar ya hankada ni waje ya ja motarsa ya tafi abinsa.



Ba ni da kudin da zan karasa gidanmu, amma ba gida nake so in je ba dan na san iyayena sai sun kusa kashe ni idan su ka ji abin da na aikata. Ba ni da kudin motar da zan koma Jos, na bar wayata a gida balle in yi wa makwabta waya in ce su kula da yarana kafin in zo. Sai a lokacin na kula ashe ba ni da riga a jikina.

Allah sarki! Ashe ma Isah mahaifina ya zo dubawa za a yi masa tiyata, bashi da kudin da zai biya tiyatar shi ne ya tafi ya dauki fasinja don ya cika.



Allah ya wadaran irin wannan mummunan kishi da zargi da mu mata muke yiwa mazajenmu suna ta kokarin ciyar da mu da dawainiyar yara har da iyayenmu, mu muna yi musu mummunan zato. Sai da na nemi taimako daga bayan Allah aka hada min kudin mota, dakyar na samu na dawo Jos na samu makwabciyata ta dauko yarana ta rike ashe tunda safe Isah ya yi musu waya ya ce su kula da yara. Na yi iya kokarina na bashi hakuri ya ce ba zai zauna da ni ba, na fi shekara a gidanmu sannan ya yarda ya mayar da ni bayan ya dankara min kishiyoyi biyu na zo na zauna a ta uku.


Daga Jamila Umar Tanko (JUT)

0 Comments: