Headlines
Loading...

KIMIYAR MAGUNGUNA NA


Kanumfari:


Kanumfari yana ɗauke da sinadarai masu matuƙar alfanu da muhimmanci ga lafiyar ɗan-Adam. Ga wasu daga cikin alfanun kanumfari:


1. Kanumfari yana inganta lafiyar ƙwaƙwalwa. 

2. Rigakafi ne dangane da kamuwa da gyambon ciki.

2. Yana daidaita sikari. 

3. Garkuwa ne ga kamuwa da sankarar nono.

4. Yana kassara kwayoyin cututtuka da kashe su.

5. Yana taimakawa wajen rage teɓa.

6. Yana inganta kwayoyin haihuwa.

7. Yana takmakawa wajen mikewar alƙalami.

8. Yana sanya kaifin ƙwaƙwalwa da hazaƙa.

9. Yana hana saurin izali.

10. Yana inganta kwayoyin mace da maniyyin namiji.

11. Yana maganin ciwon mara lokacin al'ada.

12. Yana maganin saurin tsufa.

13. Yana maganin jiri.

14. Yana kara alherai ga mace.


Alfanun kanumfari ne ya sanya a dauri ake sanya shi a cikin abubuwan ci da sha.


Fadakarwa: Ba a mayar da kanumfari ruwan sha ko a cika shi a rinka sha kullum kamar yadda mata suke yi a wannan zamani yin haka yana da illa. Matukar za a jika shi, to, sai dai a rinka shan sa jefi-jefi kuma saisasaisa. Idan kuma kullum za a yi amfani da shi a sha, to, kada ya haura kwara 4 zuwa 5 ko 6.


Fa'ida: Idan aka haɗa kanumfari da saiwar zogala guda 7 da domashi guda biyar da benidazugu saiwa biyar da saiwar hankufa guda uku da tsintsiyar maza sala 7 yana maganin gyaran danga sosai matuƙar raunin mutum bai jima ba, idan ya jima, to, a gana da masana lafiya, kada mutum ya zama likitan kansa. Kuma kada a mayar da shan wannan haɗin kullum.


Daga Abu Razina Nuhu Ibrahim Paki

0 Comments: