Kashin Kai ya kauda Rotse!
Mutun yaci Biredi Yana hadawa da shayi, Amma idan ya gama sai yace Maka "SHAYI NISHSHA" to shi biredin fa?
Ka ci tuwo ka Sha Miya, amma idan ka gama kace "Tuwo Nicci"
Duk da masu kurin Hausa sun kasa banbancewa tsakanin "Dawo" da "Fura" saboda shi gululun dawo kafin a dama shi da Ruwa da nono Sunan shi "DAWO" idan Kuma aka hada shi da Ruwa da Nono aka dama ya zama "Fura"
Sai dai na rasa dalilin Bahaushe da yake Kiran Mutun Marar wayo da Sunan "DAWO"
"ROMO" kamar Ruwa yake Amma shi Sharbar shi ake Yi, su Kuma Ruwan Shan su ake Yi.
Ma su magana sai sauce za kusha romo da nufin za kuji dadi, amma idan Mutun yayi magana wadda ba tayi daidai ba sai ace ta bashi Ruwa.
Tau shi lamarin duniya dai Dan hakuri ne, Kuma Dan juriya ne. Sa'a ta fi sammako, Kuma abu ga Allah ake Neman shi sai ka zauna lafiya.
Boka makaryaci ne, komai ya Fadi karya ne, in ba abunda ya zamanto na zahiri ba ko abunda ya tabbata ga addini ba. Misali yace Allah guda ne, zaka yadda. Ko yace bayan yini dare zai zo da dai sauran su.
Lakcha ce kawai da Falsafa ta mutanen da suke son ganewa.
Barkan mu da hutun karshen Mako.
0 Comments: