Headlines
Loading...
Ingatattun Hanyoyin kasuwanci, ba Novels ba

Ingatattun Hanyoyin kasuwanci, ba Novels ba

Ingatattun Hanyoyin kasuwanci, ba Novels ba


Bayan tela, masu shagunan tireda su ma suna bukatar sanin hanyoyin kasuwanci.


Shafin uwar gulma ya dauki aniyar warware maku sirrin nasarar kasuwanci da kuma mutuwar kasuwanci, uwar gulma ta gama aikin ta, saura kai.


Shin kana cikin masu yiwa budurwan unguwarku hidima? Ka zama bestie kaima.


Domin in taimaki rayuwar ka ni "uwar gulma na gwangwaje ka da wannan bayani.


Na ta'ba cewa wani ina sha'awar bud'e shagon tireda. Kawai sai yace mini lallai, ai they are not growing. Ma'ana, wai harkar tasu basa cigaba. Idan ka san tireda shekaru 10 baya, to galibi yadda ka san shagon nasa tun wancan lokacin, to babu abinda yake qaruwa. Sai dai ma qila ka ga yayi qasa, ya dakushe. 


Gaskiya ne wannan. Amma matsalar ba daga kasuwancin tiredan bane, daga rashin sanin hanyar kasuwancin ne. Matsalar daga masu shaguna ne. Galibinsu basu da Financial Literacy ne, kuma kasuwancin kawai suna yi ne. Amma wadanda suke da Financial Literacy, to suna bunkasa. 


Sai ka ga mai shago yana saida kaya. Amma a karshe  idan ya tara kudi, baya iya ware riba daga asalin jarinsa. Wanda kuma yake iya ware riba, sai ka ga bai san cewa ba duka riba ake kwashewa a ci nama da kaza ba.


Yanzu misali



mai shago ne yake saida ruwa "pure water". Sai ya siyo jakar pure water mai guda 20 akan N160. Ka ga kowani pure water N8 kenan. Shi kuma yana saidawa akan N10. Ribarsa akan kowani pure water shine N2. 


Amma sai ka ga an zo siyan pure water guda biyu kacal, masu sanyi. Sai kuma ya sanya a cikin leda. 


Asalin ribar saida wadannan pure water guda biyu shine N4. To, yanzu a N4 dinnan, nawa ne kudin leda? Nawa ne kudin wutan lantarkin da aka sanyaya wadannan ruwan? Nawa ne kudin hayan shago? Sannan shi mai shagon, nawa zai saka a aljihunsa a matsayin ladan hidima?


Duk fa wannan ya kamata ace an lura da su wajen saita farashin saida kaya. Duk kayan da kake saidawa, dole ka zauna ka masa irin wannan lissafin domin ka gane hakikanin abinda kake yi. Shin kasuwancin nemawa kanka mafita kake yi, ko dai hidimar unguwa kawai kake yi ba tare da kayi niyya ba. 


Wani kuma idan ya bude shago, haka zai ta bada kyaututtuka babu lissafi. Ko kuma shi da kansa ya zauna yayi ta cin dadi. Ya sha madara, ya aikawa mai shayi kwai 3 a fasa masa, kuma a soya mishi Indomie 2. Toh, galibi kayan tireda ribarsu babu yawa. Don haka duk lokacin da ka buga sharholiya iya sharholiya, to ba mamaki ka cinye ribarka ne na wata daya. Kila ma har ka fara cin jarinka.


Shi yasa kake ganin mutane da zaran sun bude shago, tun kafin aje ko'ina sai su rufe shagon. Babu proper book keeping ne. Matsalar ba daga harkar tiredan bane. A'a. Kawai awon igiya ne yayi yawa a ciki. 


Abin mamaki shine


Yau a duniya kamfanin da ya fi kowani kamfani samun kudaden shiga (revenue), harkar tireda ya fara da shi. Kuma har yau dinnan harkar tireda yake yi. Wannan kamfani shine kantin Walmart. Sun fara harkar tireda tun a shekarar 1962, kuma har yau harkar suke yi. Sun zarcewa kowani kamfani wajen samun kudaden shiga. A wannan duniyar da ake da kamfanonin mai irin su Saudi Aramco da Shell da NNPC. A wannan duniyar da ake da manyan kamfanonin kimiyya irin su Apple, Alphabet da Meta (Facebook). Duk ace kamfanin da ke harkar tireda ya fi su samun kudaden shiga! Kantin Walmart sun fi kowa karfin kudaden shiga. 


Walmart ai sun fara ne da wani dan karamin shago a 1962, a jihar Arkansas ta kasar Amurka. A hankali suka yita ririta abinsu har gashi yau sun fi kowace kamfani karfin kudaden shiga. Ashe kenan harkar tireda harkar kwarai ce. Sai dai idan ba a yi shi da kyau ba, ko kuma qaddara ta riga fata. 


Sanin hanyoyin kasuwanci nada matukar amfani domin bunkasa kasuwa.


Allah ya sanya mana albarka a nemanmu, Amin. 


- Ibrahiym.

0 Comments: