Headlines
Loading...

Halayen dake haddasa lalacewar Koda

Daga Dr. Ibrahim Y Yusuf


Ƙoda abace mahimmiya kamar yadda nasha fada, infa ta sami matsala toh babu sauran labari, lokaci kankani cikin wata 3 kana iya zamowa tarihi, domin galibi tana da kokarin gyara kanta inta sami matsala, amma zarar matsalar takai ga bayyana tohfa lokacin an makaro. Ƙoda da kake gani tana kuka tai hawaye kamar yadda kake hawaye in andokeka kaji zafi ita.


Kai tsaye aikata wadannan ɗabi'un ga mutum ba abune mai kyau ba ga ƙodarsa... don haka inkaji ko kinji wani abu da kunsan halinku ne to ku daina kurum.


Yawan Rikon fitsari

Jinkiri wajen yin fitsari cutar da Kaine mutum ya kasance duk sanda fitsari ya kamasa yanajin amma yaki zuwa yayi saide yaita rikon sa yana takurewa, hakan ganganci ne babba. Kusani duk sanda ƙoda ta tace fitsari ta turo shi ga mafitsara ba abunda da akeso irin afitar dashi domin inkana rikeshi to ahankali wani zai fara komawa ga ƙodar (reflux) wanda daga nan kuma matsala zata fara afkuwa.


Yawan amfani da gishiri

Yawan shan gishiri akwai matsala ga ƙoda basai ga mai hawan jini ba, musamman mutanen dake da irin dabi'ar nan ta karama abinci ko Miya danyen gishiri saboda bai musu daidai ba, kome so suke sujisa zau ajika! In gishiri yai yawa ƙoda bata iya tsotse daga circulation baki daya zai mata yawa bayan ya illata ta dole ta sakesa yaci gaba da yawo ajika wanda hakan matsala ne.


Matsala ne tunda zaisa pressure ajijiyoyin jini ya qaru abunda ake kira hypertension shiyasa hatta masu hawan jini abu na farko zakuji da ake fadamusu su kiyayi gishiri da dangoginsa su maggi saboda ba jinin ba kadai hatta kodarsu don karta lalace, domin duk mai hawan jini ko ciwon suga na cikin hatsarin ciwon koda inbai kiyaye ba. 


Don haka a kiyaye tunma ba in mutun cikin mahaifansa dama akwai mai hawan jini ko ciwon suga ba saboda kaima kana iya wayar gari dashi akoda yaushe.


Shan Magunguna ba kan ka'ida ba da rashin daukar ciwo da muhimmanci

Rashin daukar kananun cututtuka da mahimmanci wanda mutum ke ganin ko ba'a je ga likita ba xa'a warke kamar jin ciwon kuiɓin, zafin fitsari, ko fitar farin ruwa daga gaba, ko mura wacce daga karshe aka kaiga jin kaikayin makogoro duk mutum yai watsi dasu... har suci suci su bari. 


Ko ya zamto mutum ya zama shine likitan kansa saide yaita dannawa jikinsa magunguna antibiotics ko NSAIDS daka ba tare da shi kansa yasan menene taka maiman matsalarsa ba shide shan magungunan kurum yake ba bisa kaida ko umarnin likita ba. Musamman Mata masu ciwon mara yayin haila, ko kaji wata har recommeding ma wata magani take akan aini magani kaza nake sha kema ki nema kisha... ko kuma mutum yaje yaga likitan ma amma yazo yana shan maganin ba yadda likita ya tsara ba....


Wadannan halayen na cutar da ƙoda kwarai da gaske don haka duk mai irin wannan Shima ya kwan da sanin yana mikawa ciwon koda katin gayyata duk randa akace an fara samun angwada jininka creatinine yai sama, ko angwada fitsarinka ansami proteins, glucose ko jini aciki to karkai mamaki kuma alamace ta ƙoda ba lafiya.



Sannan kananun jami'an lfy wani lokacin kuna taimakawa wannan barnar mutum baisan pharmacotherapeutic dynamic da kinetic effect na magani ba kurum symptoms din da yake kawarwa ya sani amma sai yaita rubutawa marasa lfy batare da binkitar ko da taya ciwo ko matsala ta faro ba, hakan na qara cutar da mara lafiyar batare da saninsa ba 


Kananun jami'an lafiya ai aiki bisa  lura da amana in baka da training ko kwarewa akan bada magani toh kabar aikin ga masu shi ko ka tura mutum ga babban asibiti yafi. 


Domin akwai wanda already kodarsu ta fara failing zasu zo amma abunda tazo korafi akai kila shine ciwon mara... kai kuma ka dau maganin rukunin masu rage zogi ko zafi ka bata wato irin ibuprofen, feldin, diclofenac ko aspirin ka bata... ta tafi taje tasha taji sauki, amma azahiri wadannan magungunan da take cigaba da amfani dasu kara lalata mata koda suke amma saboda ciwon koda bai bayyna lokaci guda sanda ciwo zai zo ya kwantar da mutum sannan an makaro.


Wani zaizo yace ma ciwon hannu ne ko kafa kai tsaye ka bashi maganin ciwon jiki amma ainishin matsalar ba anan take ba, referred pain ne, matsalar ciwon zuciya ce ke alarming a hannunsa amma baka sani ba, wano kirjin ne zai zo yana ciwo.... ka zaci ulcersa ce ainishi shima kila already heart attack yake fuskanta sai ya tafi kwana daya biyu ace ya mutu arika ciwon ulcer yai.



Wani kuma zaizo ciwon daga tsakiyar cibiya yake... zaice ma ciwon ciki ne kurum, kila kai ko tambayar daga daidai inda ciwon yake ma bakai ba, shide yace ciwon ciki, sai kuma amai ko tashin zuciya kai kuma ka dau maganin ciwon ciki ko ulcer ka bashi babu binkice ya tafi yaje gida ya kwanta karshe ya mutu..... alhalin appendicitis ne yake damunsa sakaci da rashin sani aikinka yasa yasa appendicitis din yai distention yakai ga fashewa infection ya watsu acikinsa yabi jini kafin aje ko ina ya mutu.


Wani ciwon kafa ne zaizo da ita amma azahiri ciwon sugar ne dashi wanda shi kansa bai sani ba, ciwon kafar already complications na diabetes kaga ko ka bashi magani yaita dawowa kenan domin maganin ciwon kafa kake bashi bawai maganin matsalar ba. Wani kuma zai fadama yana da ciwon suga amma kila tunda ba abune da aka koyar dakai ba bakasan kome game da abunda sugar zata iyayi ba don haka zakace bari zan baka magani, ka gabza masa Nsaids ya tafi karshe ashe babu ma blood supply kafin a farga wani sashi ya fashe kafar ta fara rubewa ta ciki tana bushewa ta waje karshe sanda za akai ga manyan likitoci saide ai zancen yanketa.


Don haka likitanci yana da fadi, a wannan gaɓar kananun ma'akatan lafiya dole sai kun lura, ya dace gwamnati tai tsari da za ake karamuku sani, domin musamman a yankunan karkara gaskiya kymune kukafi kusa da mutane saide gashi kuna missing din medical cases da yawa wanda wasu mace macen ana iya kauce musu.


Kada kuke sake wajen tura mutum ga manyan likitoci in abu yafi karfin fahimtarku, sannan kada ko yaushe kake kankanta ciwo matsayinka na karamin jami'in lfy ba haka abun yake ba, inakyi sau 1 aka dawo toh na biyu kurum fadamusu abun ya wuce tunaninka amma ga shawara suje asibiti iri kaza da kaza suga babban likita kurum.



Yawan cin nama Ja


Yawan cin Nama fiye da kima kullum kullum, ko akai-akai ba birgewa bane inde don ka damu da lafiyarka ne. Masu wannan dabi'ar su sani cewa ba burgewa bane ace kamai da cin Nama kullum kullum ko kuwa kwana 1 ko 2 kurum kake daga kafa musamman naman shanu, raguna kai har na kajin ma. Hasali ma Kila baka ko baki da kokarin motsa jiki, Mutum inya samu abu sai yaji yaci-yaci yai hani'an toh hakan ba abune mai kyau ba mutum ya kiyayi kansa.


Rashin cin wadataccen abinci


Rashin cin wadataccen abinci matsala ne, Haka kurum bawai babu ba, amma mutum ya rika ma kansa kwauro da gangan Saboda tsurfa ko kuwa tunanin kar yai kiba, bazai saki jiki yaci abinci ba ko kuwa yaci yadda ya dace har sai ya fara ganin jiri to masu irin wannan suma su kuka da kansu kodarku na iya lalacewa akoda yaushe. Ina nan da rubutu kan masu wannan halayyar takin cin abinci wai don tsoron karsui kiba.


Rashin shan ruwa wadatacce


Rashin shan ruwa wadatacce yadda ya kamata babbar matsala ce ga jiki, lamba 1 ma kuwa. ya zamto mutum yana jin kishi sai yasha kadan ko kuwa ma mutum ya gama cin abinci amma yaki shan ruwan kwata-kwata haka kurum don wani dalili na kansa na shirme da cutar kai. 


Masu irin wannan hali su Kuka da kansu shi ruwa anso kake shan sa basai in kana jin kishi bama, kuma irin wadannan ne insukaje kashi da zaka matsa kusa da bandakin saika rantse Mace ce ke nakuda, nishi hadda wayyo, ko mutum ya rika ciccije baki yana yunkuri, kai wani lokacin sai sun sa hannu sun kamo kashin sun jawo da kansu galibi saboda they are constipated.. akan me irin wannan shirmen. 


Don haka kake shan ruwa kuma.da kaji toilet ko fitsari to babu jira maza ka tafi kayi, sai kaji kayi tsugunonka cikin sauki, amma daga lokacin da kake jin kashi ka matse kaki zuwa kayi toh inkaje yi agaba dole kasha wuya.


A karkashin wannan rashin shan ruwan ga kuma karin wasu alamomin da zaka gane lallai baka shan ruwan isashshen ruwa:



Manyan alamomi Biyar dake Nuna baka shan wadataccin ruwa


  • Raguwan adadin fitsari


Lafiyayyen Mutum akalla kanyi fitsari sau 6 zuwa 7 arana (akalla yawan da yakai kofi 3 zuwa 8 kenan) arana. Don haka daga lokacin da kaga ko kikaga kin koma fitsari sau 1 zuwa 3 arana wannan alamace dake nuna ba'a shan isashshen ruwa kuma kodar mutum na cikin mawuyacin hali.


  • Bushewar fatar jiki


Karancin ruwa ne kan gaba cikin abinda kan jawo bushewar fata aga har furfuri take, mutum zaiga komi man da zai shafa jimawa kadan zaiga ta daďa bushewa, ko kuma yaga inya jawota ya tale irin yadda likitoci ke dubawan nan... zata dau fiye de sekonds 10 bata gama komawa daidai ba... don haka sai akula. 


  • Yawan ciwon kai


Rashin shan isashshen ruwa na jawo ciwon kai, irin ciwon kan da akan jisa haka kurum batare da zazzabi ko jin tempreture jiki tai zafi ba, kuma babu wasu sauran alamu kawai suddenly akaji ciwon yazo kai yahau harbawa toh karancin ruwa na janyo hakan... musamman in mutum ya zamo busy so stressful hakan bai rasa nasaba da karancin ruwa ajiki.


  • Bushewar fata baki

 

Bayan bushewar fata a wasu lokutan akanji miyau ya dauke abaki gaba daya, ko bakin mutum har yaji ya rika ďaci ko jin kamar wani lump ya tsaya masa awuya wannan ma na daga alamun rashin isashshen ruwa ajika. 


  • Chanzawar launin fitsari


Wato inma de kana iya yin akalla mai yawan da yakai kofi 3 zuwa 5 ayini toh amma sai ya zamto kalarsa ta canza kamar yadda zan bayani akasa toh hakan na nuna jikinka ya raina ruwan da kake sha don haka ba yawan fitsarinka ne ma'auninka ba... A'ah da kalarsa za kake tantance kanka. Saboda wasu suna da kibar da suna bukatar shan ruwa sosai... wasu kuma metabolism dinsu ne mai zafi.


Fitsarin lafiyaye mai isashshen ruwa ajika ya kamata ya zamo clear wato kaga fitsarinka kamar kalar ruwan da kasha ko kuwa ya zamto launin ya canza kadan zuwa amber color amma ba sosai ba. 


Kamar yadda hoton kasa ya nuna launi hawa-hawa har uku "3" na yadda fitsarin mai shan isahshen ruwa (Hydrated), mai karancin ruwa (Dehydrated) da kuma mai tsananin karancin ruwa (extremely dehydrated) suke. 


Gargadi

Kasani kamar yadda in andakkeka kaji zafi kake kuka haka fa kodarka ke kuka inka qi shan ruwa ko inta sshig mawuyacin hali, tana yin duk yadda zatai ta kwaceka amma in abun ya zamo halinka kullum-kullum tohfa karfinta na tafiya daga lokacin ta rasa lafiya kuma da wuya likitoci su iya cetoka sai anyi da gaske umba sa'a ba tafiyarka tazo. 


Domin kamar yadda nace koda tana lalacewa to ko inafa ajikinka sai ya lalace... bar ganin amfanin zuciya... in koda ta lalace tafita hatsari, domin zuciya zata iya dan aiki na wasu kwanaki kafin ta tsaya cak... koda kuwa kai tsaye zata kasa tace komi daga nan gubace "uremia" zata fara zagayawa cikin jininka tunda koda ta gaza taceta tana shiga kwakwalwa shikenan ka gama yawo kwanaki kadan inba ai komi ba mutuwa zakai kuma saika rika abubuwa tamkar mai ta6in hankali kafin ma ka mutu abunda muke cewa uremic encephalopathy... Mutum yai hankali da kanshi. 


Yanzu jikkunan mu bafa irin na iyaye da kakannin mu bane, bamu da inganci irin nasu dam, saboda su sunyi ciye-ciye daidai da jikinsu irinsu (kwadon rama zogale, dinkin, dawa-da kulli, burabusko, kunun tsamiya, tubani, natural fura da nono, zuma mai inganci, nama mai inganci, suna tafiyar kasa me nisan gaske, man kadanya, man zaitun da sauransu) shyasa suka zauna lafiya.


Amma mu yau in ma munce zamuci irin nasun toh sai mun kashe abun yadda bazai wani aiki ajikin mu ba sannan mutane ke ci wai su wannan shine daďin (kaga zogale duk an gabza masa yajin magi da mangyada, da tarin tarkace na banza taya zaka sami amfanin zogale da akace? Haka ma dan wake za'a gabza masa hade-hade da duk amfanin nasa da za'a samu angama lalatashi shiyasa da mutum ya gama ci sai kashi da gudu zuwa ban daki.


Ciye ciyen mu duk tarkacen banza yafi yawa kadan ne masu cin abunda zai fishesu. Su pizza, chocolates, wainar fulawa, shinkafa ma sai antoyeta ko an mata dahuwar da baza asami wani fa'ida ba saide mutum yaci glucose kurum, taliya sai an lalatata, su indomie din nan, toyayyen kwai wani yamai dashi kullum.


Kuma kunsan wani abu wani nashan kayan maiko rukunin protein amma zakaga yana shan tea.. kaga anyi ba aiba? Domin sinadarin dake jikin lipton bazai bari ka amfanu da protein din ba. Shiyasa karshe saide ka tara kitse, in namiji kaga yana tumbi, Mace kuma kaga tana aje duwawu duk su dauka lafiya ce bayan jikin ku ne ke muku warning cewa abubuwa basa tafiya daidai ku dau matakin gyara kafin jijiyoyin jininku su fara dodewa ku shadu da mugun hawan jini da atherosclerosis da zai shutdown din kodarku...


Muhimman shawarwari.

Shifa jikin dan adam yanason service da kulawa kafin ya zauna da lafiya kamar yadda Mota in ana mata juye tafi lafiya. Don haka jiki ma na bukatar hutu, wanka, sanya tsaftataccen tufafi, ruwa da kuma abinci mai kyau ba mai tsada ba.


  • A daure ake shan isashshen ruwa musamman lokacin da aka fitar da zufa sosai ko lokacin zafi, haka har lokacin sanyi koda kuwa ba'a jin kishi saboda jiki nason haka, kuma adaure da asuba in antashi ake fara shan ruwa a emptyn stomach kafin cin komi akalla kofi 2.


  • Sai wani abu mahimmi dana sha fada; musamman wajen motsa jiki, Mata aikin gida ba motsa jiki bane musamman ga mata, akoyi yin tafiyar kasa wacce zuwa da dawowa batafi minti 30 zuwa 40 kar ace kullum saide ahau abun hawa, arika motsa jiki, akuma ke cin abinci mai tsafta, adena yiwa girki ko vegetable hade-hade.


  • Cin ingantaccen abinci mai kyau bame tsada ko hade-hade ba, Jikinmu mu bakar fata bafa daya bane dana turawa, karku rudu da cimar wasu ku saki taku baza kuga da kyau ba. Suma turawan yanzu babbar masifar dake damunsu bakamar cutar teɓa wato obesity... Akalla duk mutum 2 cikin 3 nauyinsu ya wuce ƙima, ..
  • Muma yanzu haka akwai tarin overweight kuma inbakui hankali ba toh duk hakace zata faru daku, ba zakakewa cikinka zube-zube ba kace kuma kanaso ka zauna lafiya kamar yadda kaso... 


A tarihin likitanci bamu ta6a ganin wani mai kiba ko overweight da ya rayu kusa da shekara 100 ba aduniya. Don haka idan kanason rayuwa mai tsayi cikin inganci to kayi cima me kyau.


  • Ake cin fruits da vegetables, da koyar canza abinci. Yana da kyau karka maida cikin ka koda yaushe abinci iri guda kake zuba masa wato kaita cin abinci maisa kuzari kullum ko mai gina jiki kurum.... jiki bayason haka shiyasa masu yawan cin abinci maisa kuzari batare da aikin komi ba kanyi fama da te6a ajika domin abunda kakeci baka iya aiki ko matsa jikin da zaka konesa.


Abinci maisa kuzari shi ake kira (carbohydrates) wato inkana cin wadannan abincin; Masara, tuwo, dankali, shinkafa, doya, macaroni, spaghetti, roogo, garin kwaki, wainar fulawa, cin-cin da duk wani abincin flour ko hatsi.... Abu daya fa kaketa ci kullum domin duk carbohydrate ne sunane kurum ya bambanta amma aciki duk abu daya zai zamo... wato glucose ya baka kuzari akarshe wanda baka iya konewa ba ya zamo kitse aturosa kasan fatarka aga kafara kumbura kana kiba...  don haka ake gaurayawa da vitamins na fruits, vegetables, protein su kifi, wake, awara, dafaffen kwai da sauransu jefi jefi duk sanda aka sami iko basai kullum ba.


  • Ake fita fitsari akan kari da zarar anji alamunsa.


  • Da anji ko anga alamun cuttukan sanyi wato kaikayin gaba, ko fitar farin ruwa agaba ga mace ko namiji anemi magani, haka ciwon makogoro bayan mura.



Dauki mataki



  • Yawan ciwon baya ta kuɓin ciki daga kasa sama da ƙugu kadan ko sama zuwa kafada,
  • Canzawar dandano abaki zuwa kalar kanwa ko kamar ansa karfen da yai tsatsa ko lamba abaki
  • Canzawar fitsari zuwa duhu kuma aga yana fita kadan-kadan in anje yi,
  • Yawan ganin jiri da kasa sukuni,
  • Yawan kasala
  • Ganin kuraje ajika wanda da anshafa magani zasu 6ace amma su kuma dawowa.


To ahanzarta zuwa aga likita domin wadannan na daga alamun ciwon koda.


Fata anji za kuma akiyaye umba haka ba, toh gadajen mu de na asibiti ko yaushe suna maraba da mutum, kazo ka kwanta in abunda ka tara ya qare a neman lafiya daga nan likitoci suka kasa cetoka kaga sai ka wuce lahira ka huta.


Daga Dr IbrahimYusuf

0 Comments: