Headlines
Loading...

 HUKUNCIN SHAYAR DA NONO.


Akwai al'ada da musulunci ya tarar ana yi ta shayarwa da ake tsakanin al'umma, shine a ɗauke yaro daga wajan mahaifiyar sa a kai shi wani waje wata mata ta shayar da shi, asali mahaifiya (uwa) ya kamata ta shayar da ɗanta, idan ba wani dalili ne ya faru ba, kamar mutuwa ko rashin lafiya, ko rashin nonon da za a shayar, ko kuma al'ada kamar yadda Larabawa suke kai ɗansu kauye a shayar da shi, domin ya taso da fasaha juriya, irin na mutanen ƙauye, kamar yadda ya faru ga Manzon Allah saw, Halimatu Saadiyya ta shayar da shi bayan mahaifiyar sa da kuma suwaibatu al'aslamiyya, an shayar da shi tare da Hamza da Abu Salamata, shi ya sa yake kiran su ƴan'uwansa na shayarwa. 

Bisa haka musulunci ya bayyana hukuncin wanda aka shayar da shi, nono wanda ba na mahaifiyar sa ba. Suratu Nisa'i aya ta 23.

Idan mace ta shayar da yaro ko yarinya, wannan matar ta zama uwa ta shayarwa garesu.

Don haka sai a kirawo wannan matar uwa ta shayarwa. Saboda hadisin da yazo an bawa Manzon Allah saw shawara ya auri ƴar sayyadina Hamza RA, sai yace :Bata halatta a gareni ba, saboda  mun sha nono tare da mahaifinta, kamar yadda ya haramta ka auri makusantanka na jini, haka ya haramta ka auri wanda ku ka sha nono tare, sai aka duba aka ga wacce ta shayar da kai ta zama mahaifiyar ka ta shayarwa. 


WAƊANDA YA HARAMTA A AURA SABODA HUKUNCIN SHAYARWA.


Yazo a cikin Alkur'ani mai girma aya ta 23, sura ta 4. 

"DA KUMA BABANNINKU WAƊANDA SUKA SHAYAR DA KU, DA KUMA ƳAN'UWANKU NA SHAYARWA " NISA'I AYA TA 23. SURA TA 4.


Manzon Allah saw yace : Shayarwa ta na haramta irin abinda nasaba take haramtawa. Bukhari 5099.Muslim. 1444.


Duk matar da ta shayar da mutum nono ta zama babarsa ta shayarwa sai a kira ta :

1 Mahaifiyarka ta shayarwa

. 2 Mijin ta ya zama babanka na shayarwa

3. Ƴaƴanta sun zamo ƴanuwanka na shayarwa

4. Ƴanuwanta sun zamo danginka na wajan uwa ta shayarwa

5. Ƴanuwan mijin ta sun zamo ƴan uwan mahaifin ka na shayarwa

6. Jikar ta ta zamo ƴar ƴaruwarka ta shayarwa

7. Babanta ya zamo kakanka na shayarwa

8. Ƴar ɗanta ta zamo ƴarɗan'uwanka na shayarwa

9. Ƴar'mijinta ta zamo ƴar babanka na shayarwa

10. Matar mijin da ta shayar da kai ta zamo matar babanka na shayarwa

11. Matar ta zama haramun ga mijin matar da ta shayar da kai domin matar ɗansa ce na shayarwa.

Dalilin haramcin shine shan nono ɗaya, da zarar mace ta shayar da kai, to ta zama babbar ka ta shayarwa, kuma matsayin kamar babarka da ta haife ka. Mijin ya zama kamar babanka da ya haifeka, haka danginta da dangin sa.

Allah ya kara mana sani mai Albarka

0 Comments: