CIWON OLSA
Ciwon ulsa babbar alamarsa shine jin ciwo ko zafi a tsakiyar ciki zuwa tsakiyar kirji, saide akwai cuttuka da yawa na ciki daka iya farawa suma da ciwo atsakiyar ciki ko kirji
kamar tsakuwar matsalmama (Gallstones) musamman ga masu yawan Shan ganyen tea, ciwon saifa (spleen) ko ciwon pancreas, ciwon ƙoda, koma karamin bugun zuciya wato mini heart attack, wanda karshe sai mutum yaje yaita shan maganin ulsa yaji ba sauki sakamakon rashin sanin ainishin inda matsalar take.
A wasu tsananin ulsa takan kai ga rarike bangon cikin wato "perforation" dole sai anyi operation angyara wajen wannan ke hana ciwon Jin magani musamman inya haɗu da kwayar cuta. Shyasa ake endoscopy a hasko ciki kamar yadda yake a hotunan kasa.
MEKE KAWO OLSA LIKITA ?
Kamar yadda nace ulsa anfi Jin ciwon daga kirji ko tsakiyar ciki wajen cibiya saboda Kowanne mutum yana da wani ruwan acid da cikinsa ke samarwa (hydrochloride acid) domin narkar da abinci, toh amma a wasu mutane jikinsu na samar da wannan acid din fiye da kima wanda hakan kesa acid din ya yiwa bangon cikinsu illa saboda zafin acid din, sannan bangon cikin baida kwari sosai.
Ko kuma ulsa ta samu a saboda kasancewar wasu kwayoyin cuta na bacteriya da ake kira (Helicobacter pylori), wadanda dasu da acid din sukan hadu su kawo rami, rauni, gogewa, kwailewa, ko kwarzane a bangon cikin (stomach rugae) wanda wannan raunin da suka samar shi ake kira da ulsa ko gyambon ciki.
Wanda inba a dau mataki ba wannan kwayar bacteria din ka iya haddasa cutar kansar uwar hanji (Gastric cancer)!
Hakan olsa ba yunwa ke kawota ba, inka cire batun kwayoyin cuta ko wani magani da mutum kesha na ciwon jiki (NSAID) dakan haddasa ta... akan zargi yunwa saide sarai daci shine kan gaba wajen sa jiki ya sako wadancan hydrochloride acid din fiye da yunwar.
Domin daga lokacin da kaga wani abinci da ya baka sha'awa kakeson ci amma kuma baka cin ba, babu Hali, ko kuma ka zauna kana tunanin yau abu kaza ya kamata naci inama zan samu alhalin kuma cikin cikinka babu komi, baka ci komi ba empty yake ko sai ruwa...toh awannan lokacin kwakwalwa zata sa jikinka zai fara aika sakon sakin wannan sinadarin domin yazo ya narkar da abinci domin azaton jikinka ka riga kaci wannan abun da kake zaman tunani.
Don haka acid din zaizo ne da niyya narkar ma da abincin domin amfanin jikin, saide ayayin da acid din ya zuba sai ya tarar babu wannan abincin da yake zato
Saboda haka sai sinadarin ya zuba a bangon cikin wanda in ya zuba tamkar ka karawa fata garwashen wuta ne ko ko ince tamkar ka ɗiga dalma akan fata ne, hakan shi yake samar da kwailewar bangon cikin wanda idan hakan yaci gaba da faruwa har karshe gun ya zamo gyambo ya haifar da abunda ake Kira ulsa disease.
Kunga kenan kwadayi akai akai shike jawo ulsa ba yunwa ba! baya ga shigar kwayoyin Helicobacter wanda aka iya sha a ruwa ko gurbataccen abinci.
Barin ciki ba abinci kan zafafa wannan ƙuna na acid akan ciwon tunda idan akwai abinci a cikin acid din abinci zai ta6a ba bangon ciki ba. A wasu lokuta kuma ba gyambo haka kawai yawan acid din ke kawo kunar zuci.
Saide a wadanda tai kamari akan ga sukan yi amai hadda jini kalar coffee gami da yawan tashin zuciya.
SHIN ANA WARKEWA DAGA OLSA?
Tabbas ana iya warkewa daga wannan matsala idan mutum yaje aka duba shi aka tabbatar ita olsar ce, musamman akwai gwaji ake domin a bambance bacteria ce ko kuwa acid ne ke jawota.
Inda nan za'a dora shi a magunguna da suka dace da abunda ya jawo ulsa dinsa na tsawon makonni ko watanni tare da bashi shawarar ya kiyaye ka'idojin ta. A wasu sai an sa kyamara an haska an gani ko gymabon ne ko wani abu daban (endoscopy).
Domin ba duk ulsa ce ake shan magani iri daya ba. Kowacce da irin maganinta wannan yasa wasu sai suga tamkar maganin baya aiki. Akwai bukatar likita kansa ya tsaya yai binkice atsanake
HANYOYIN DA ZA'A BI DON MAGANCE CIWON KO YAWAN TASHINSA
1- Zaku iya shan yoghurt musamman irin probiotic dinnan, kuci naman kaji, abincin alkama, biredin alkama, taliya ta alkama, brown rice, kifi, wake, dafaffen kwai da gyaɗa dafaffiya.
2- In za'aci abinci a daina cin ɗan kadan akuma dena taqe ciki dam da abinci har arika gyatsa ana nishi, Hakan yana tada ulsa domin tamkar ka dau dutse ne me nauyi ka danne gyambon dashi. aci daidai misali.
3- A kiyaye yawan cin Abubuwa masu ɗandano sosai "Ma'ana dukkan abin da ke kama baki ajishi zau' walau sugar, ɗaci, yaji, flavor, ko gishiri kai koma de menene indai da dandano sosai.
4- A kiyaye wajen cin ganyayyaki kowanne lokaci barkatai musamman irinsu zogale, cabbage, salad, da sauransu, duk da suna da mahimmanci ajika haka kuma barazana ne ga masu ciwon ulsa cinsu ɗanyu shar saboda basa narkewa akan kari ajika, hakan kansa ciwon yana iya tashi.
5- Kuke shan nono mai kyau lokaci zuwa lokaci ko madara walau ta ruwa ko gari haka kurum basai anji alamun ciwon ba suna bada kariya.
6- A jibanci shan ruwa kullum da sassafe kafin aci komi yin hakan tabbas har ciwon nan na sankara (cancer) yana magance hatsarin sa. Hakanan akai akai
7- Idan kana da ulsa kada kake haikema aikin karfi gashi ka gaji amma ka dage saika ɗan karasa kana ganin ba yawa inkai wasa inka tintsire wataran saidai ka farko kaji ana maka sannu. Musamman yan uwana manoma, kafintoci, leburori da sauransu.
8]. Masu shafe awoyi suna bacci baya ga baccin dare (inka hada kusan baccin awa 9 zuwa 12 arana) kul kuma hakan na tada ulsa haka kuma yawan baccin nasa mutum a hatsarin kamuwa ciwon zuciya da dena sashin wani bangare na jiki (paralysis) musamman idan mutum na dauke comorbidity kamarsu hawan jini ko ciwon suga din da ake sakaci da shan magani.
Tabbas wadannan duka dokokin Olsa ne don dai kurum wadanda muka fi sani sune kiyayar Abu mai tsami, dame yaji amma wadannan ma duk sharrudanta ne
Shyasa ulcer bawai ba'a warkewa bane a'a sharrudanta ne ba yarda ka iya dole bazaka iya kiyaye su 100% ba shyasa sai de management.
Daga: IBRAHIM Y. YUSUF
0 Comments: