Headlines
Loading...

 AZIZA-11


Fuskar Nafisa ya yamutse sa'ar dataji abunda yace wani masifaffen kishi ya soki zuciyarta babu abinda ta tsana arayuwarta irin mijinta Yusuf hakanan kuma babu abinda take tsananin kishi dashi kamarsa.


Abin ya zame mata kamar jaraba, gashi dai ta Tsane shi kamar mutawarta amma da zarar ya tuno mata dalilin da yasa aka hada auren gida, sai ta ji zuciyarta na soyewa... domin ta san har yanzu ya fi son waccen tsinanniyar da ita. "To ba sai ka sake ni ba! ni nace bani sonka... kuma in kana da zuciya to yanzu ma ka rubuta min takarda ta ka bi ta can gidan mijn ka aure ta!"


"Abin da nake fata kenan a kullum". Yusif yace da ita, har yanzu hannunsa a dafe ya ke da fuskarsa, jinin ya fara tsayawa.


"Har kwanan gobe Nafisa, ban taba fitar da ran za ta fito na aureta ba, in ma gatse kike yi to kaicon ki, bakin cikin ki, domin abin da kike fadi tamkar addu'a ce a gare ni, ina fatan Allah Sarkin komai ya biye bakinki... Nafisa".


Hakan da yace shi ya dada harzukata, taji ta kuma tsanarsa, hakanan kuma kishi mai tsanani ya lulluɓe zuciyarta.


"To... to naji... in dai kana da zuciya, in kana yiwa uwarka da ubanka ka bani takarda ta yanzu ka koma gurinta. Yusif yaji wani abu ya soki zuciyarsa zai iya jure komai amma banda zagin iyaye. A karo na farko tun sa'ar da aka daura masa tanbaɗadden auren sai yaga lokaci ya yi da ya kamata ya saki wannan tsinanniyar mata. Tuntuni daman biyayyace ta sa shi zama da ita. "Ka yi hakuri Yusif, bi ta a hankali yarinya ce, za ta daina duk abin da take"

Wata kakarsa ce ta taba cewa da shi hakan sa'ar da 'yan uwa suka sa shi a gaba a ranar fadansu na farko da Nafisa. A shekara daya da daurin aurensu sun yi fada sau ashirin da takwas, ko yaushe shi ake baiwa hakuri.


Yusif ya dubeta cikin kunan rai ya ce..


"Ta shi ki hada kayanki, yan zunnan zan rubuta miki takarda". Nafisa ta mike a fusace ta nufi falo, kanta ba dankwali, rabinta tsirara tana cewa.

"Ta fi nono fari...Sai ka bita gidan mijin ka dawo da ita ta maye gurbina" Ta mako kofar dakin da karfi har dakin ya girgiza.


Yusif ya nufi kan teburi da niyyar ya dauko takarda domin akwai alkalami a cikin aljihunsa, to amma sai ya ji duk ya gaji, don haka sai ya zauna jagwaf a bakin gadon.


Hakika ya gaji da abubuwa da dama, na farko dai a yanzu ya gaji da cin mutuncin Nafisa, abaya dai ya hakurcewa izgilancinta da dama amma a yanzu bai iya jure zagin iyaye sa gashi har ta fara barazanar kashe shi me yayi zafi? Ya tambayi kansa Ba Nafisa kadai Yusif ya gaji da ita ba, hakika ya gaji da kunar zuciya kunar zuciyar da a kullum sai karuwa ya ke yi duk kuwa da cewa yau kusan shekars tara kenan da yiwa zuciyar tasa rauni "Sai ka bi ta gidan mijinta ka auro ta" wannan kalma ta Nafisa ita ta famawa Yusif tsohon raunin dake zuciyarsa, sakamakon hakan yasa jinin da ke zuba cikin zuciyarsa a yanzu ya fi wanda ke zuba kan fuskarsa


Dama ace.... Inama ace Allah ya biya bakin Nafisa hakance kawai za ta iya warkar da ciwon dake zuciyarsa ya aureta ina ma Ya dade da fitar da rai, duk kuwa da cewa har yanzu tunaninta na

nan cikin zuciyarsa kamar ma a lokacin abin ya faru. Kullum idan Yusif ya tuna da farkon al'amarin ya kan ce TSAUTSAYI 


Tsautsayi to mana. Tun da dai shekarunsa bakwai a makarantar "yan mata dake misau, amma dai-dai da rana daya bai taɓa sakin fuska a gaban kowacce daliba ba ballantana ma har a yi zancen wargi. Ya yi kaurin suna a gurin dalibai, domin bashi da wasa hakanan idan daliba tayi laifi to bulala mafi kankanta ita ce bulala biyar. Haka kawai ma babu laifin komai idan Malam Yusif ya ga dama sai yayi musu bulala. Wannan ce ma tasa har 'yan matan makarantar suka sauya masa suna suke cewa dashi Malam YUSIF ZAZZAƁI. 


Kwatsam rannan sai aka jefa Malam Yusif wani aji biyar na 'yan mata dake makarantar domin ya koya musu lissafi, domin abin da ya karanta kenan.


A ranar da ya fara koyarwa ta farko ce to tsautsayin ya afku. Lokacin da Malam Yusif ya fara rubutu akan allo sai ya fara jiyo surutu kasa-kasa daga can bayan ajin. Abin ya bashi mamaki, domin a yadda ake jin tsoronsa a makarantar ko wucewa ya zo yi ta kusa da aji sai ka ji an yi shiru. Amma abin mamaki sai gashi yau yana cikin ajin ma amma ana surutu.


Ya juyo a murtuke yana kallon daliban. "Ina shugabar daliban ajinnan?" ya tambaya wata 'yar siririyar budurwa ta mike tsaye kanta da jan dankwali. "Rubutamin sunan wacce ke surutun nan a baya, idan an koma ofis ki bata sunan a takarda ta kawomin ofis da kanta". Sauran daliban suka yi ajjiyar zuciya cikin kaduwa, lokaci guda kuma duk kawuna suka juya suna duba izuwa yarinyar da ita suke tsammanın ta yi surutun

"Yau...ta shiga uku" wata yarinya tace cikin zuciyarta Jikinta na rawa. Ya taba yi mata bulala goma.


Bayan an tashi daga makaranta sai dalibai suka yi cincirindo awata bishiya da ke can nesa da ofishin, Malam Yusif, duk sun kasa kunnuwa suna jira su ji yarinyar ta fara ihu. Yusif ya ajjiye 'yan littattafansa na lissafi da guntun allin da ya rage akan teburi sannan ya mika hannunsa ya bude tagar ofishin saboda tuni har ya fara gumi saboda zafi. Budewarsa ke da wuya sai duk 'yan matan da ke tare a gindin bishiyar suka watse cikin fargaba domin daga inda yake yana iya hangensu ta tagar ofishin. Yusif ya yiwa kansa murmushi, shi kansa yasan yadda dalibai ke tsoronsa.


Ya zauna a hankali akan kujerar dake ofishin sannan ya zaro katuwar bulalar ya dora ta akan teburin. Sa'annan ya lumshe idanunsa yana tinanin irin horon da zai yiwa yarinyar idan ta shigo, domin rabon da wata daliba ta yi surutu yana cikin aji har ya manta.


Bulala goma... wata zuciya tace dashi... a'a bulala biyar dai da share-sharen bandaki... haka dai yayi ta tunane-tunane. Har sa'ar da yaji an yi sallama.


"Salamu alaikum" wata zazzakar murya mai taushi ce tayi sallamar. Ba wai zakin muryar bane kawai ya bashi mamaki, akwai wani inganci a cikin sautin muryar da ya sa zuciyarsa harbawa, domin babu alamar rawa ko kuma rauni a cikin muryar, saɓanin sauran dalibai da idan suka yi laifi da kyarma suke iya buda bakinsu a gabansa.


Abin ya zo mishi a bazata domin bai taɓa tsammanin yarinyar da zata zo masa a matsayin mai laifin ba kyakkyawa ce.

Ya kasa motsi na 'yan dadiku yana duban hikimar Ubangiji, 'yar budurwar dake tsaye a gabansa kyakkyawace kamar balarabiya, kai ko a cikin litttafin hotuna na zaben sarauniyar kyau na kasar masar da ya taba gani, bai ga mai kyawun wannan matashiyar budurwa dake gabansa ba.


Yusif yayi mamakin kansa sa'ar da yaji ya sassauta muryarsa yace.

....kece kike mana surutu a cikin aji" Yarinyar ta dan sunkuyar da kai sannan ga dadin mamakinsa sai wani tattausan murmushi ya subuce daga madai-daicin bakinta.


"Aisha kawai nake yiwa magana, ita ma cewa na yi da ita ina sha'awar yadda kake rubutu Malam Yusif kura mata idanu a rude, shi kansa bai san abin da ya kamata yace da ita ha. To amma saboda son ya sake jin dadin zazzakar muryar sai yace. "Kuma ke wato ba za ki iya bari ba har sai an tashi ba ko?"


"Yar budurwar ta sake dubansa cikin kunya kunya dariya dariya

"Ka yi hakuri Malam, ni da na dauka idan an yabi mutum farin ciki yake yi shi yasa na fadi da dan karfi ko ka ji" Zuciyarsa ta harba me take nufi?

"Ba'a wasa a wajen karatu, in za ka yabi mutum sai ka bari sai kai dashi". Bai son ya daina jin dadin muryar so yake tayi ta magana yana saurarenta. Abin kuma da ya fi bashi mamaki shine da duk zamansa a makarantar bai taɓa sanin taba.


"Ina fatan nan gaba za ki kula, domin idan kika sake zamu gauraya dake".


"A wani abin da ban ba", "yar budurwa tace cikin zuciyarta. "Ina fatan kin gane?" Ta gyada kanta cikin gamsuwa sa'annan sai tayi abin da ba'a taɓa yi masa ba. Ta matsa kusa da teburin da yake gabansa, ta taba katuwar bulalar sannan tace.

"Kai...Malam.... Wannan idan ka daki mutum da ita ai matuwa zai yi". Sannan sai ta juya abinta tana cewa.

"Malam na gode gobe kenan idan ka zo aji..." " "Tsaya mana" Ta juyo tana dubansa cikin dan ladabi.


"Ina takardar da nace a rubuto sunanki a baki ki kawo?" "Af... wallahi mantawa na yi". Ta lalubi aljihunta, sannan ta mika masa lokaci guda kuma ta juya abinta ta nufi kofar ofishin. Yusif yayi ajiyar zuciya, lokaci guda kuma ya dubi sunan da ke jikin takardar an rubuta. AZIZA.


Ya dago kansa a dai-dai lokacin da ta kai daf da kofar ofishin, sai ta juyo suka bada ido, ta jefe shi da murmushi, sannan ta fice daga ofishin tana rausaya ta barshi a nan yana duban kofar ofishin cikin kaduwa.


To amma kuma daliban dake waje suna jiran suji ihun kukanta, su suka fi kowa kaduwa sa'ar da suka hangeta ta fito tana murmushi, hakoranta farare sol kamar gonar AUDUGA. 


******** ******** ******** ********* ***************


Labarin soyayyar Malam Yusif da dilbarsa Aziza ya fara yaduwa sannu a hankali cikin makarantar kamar gobarar daji. To dalibai na yi a Boye har suka fara fitowa fili, musamman ma ranar da aka wayi gari an tsige shugabar daliban makarantar an nada Aziza


Kwarjinin Malam Yusif ya zube a don dalibai, suka daina tsoronsa, daga Karshe kuma suka fara raira wakoki, na zambo, Wata rana da daddare Malam Yusif yaje gidan su Aziza suna hira

sai tace dashi. "Ka da ka damu da duk abin da suke yi ma... wallahi abin ma damuna domin na fahimci soyayarka da ni ta janyo ma zubewar mutunci... ka yi hakuri... In Allah ya so duk bakin cikinsu sai mun yı Aure an ga 'ya'yanmu". Malam Yusif yayi murmushi farin ciki. Bai cika yawan magana ba, ya fi so ya yi ta sauraren daddadar muryarta. A ranar a farfajiyar tangamemen gidan su Aziza suke, hasken

farin watan ya dada kawata furannin da ke zagaye da farfajiyar.


"Na manta ban fada maka ba" Malam Yusif ya dubela da murmushi

"Me kike son fada?" "Na kusan komawa garinmu, da mun gama jarrabawar karshen nan zan tafi" Ya dubeta a karo na biyu cikin mamaki zuciyarsa na bugawa. "Ban fahimce ki ba... ina kike son tafiya?" Aziza ta sunkuyar da kai tana wasa da awarwaron dake hannunta.


"Ai kasan nan ba gidan mu bane tun ina karama kanwar babata ta daukoni daga KANO ta dawo dani gurinsu, to shine babana ya aiko yace idan na gama sakandire a maida ni can, domin wai... shi a Jami'ar Bayero yake son naci gaba da karatu".


Yusif yayi jim kamar ruwa ya cinye shi, zuciyarsa ta fara kuna nan da nan gumi ya fara kwarara a goshinsa.


"Haba Yusif.....mene ne kuma na damuwa ai ba mun rabu da kai ba kenan" Aziza tace dashi lokacin da ta ga halin daya fada. Yusif ya dago kai kamar zai fashe da kuka.

"Ai dole ne na damu Aziza, domin rabuwa da ke ba karamar masifa bace a gurina...kuma..kuma... kin ga kenan a yadda kike fadi sai kin gama jami'a za muyi aure... shekaru hudu!" Aziza ta matso kusa dashi ta dafa hannunsa tace.


"Alkawari ne Yusif, duk tsanani, duk tsawon lokaci, duk nisan inda nake duk tsawon zamani, ina nan tare da kai, ai shekara hudu tamkar kwana hudu ce.........


ABINDA BAISANI BA SHINE.....

0 Comments: