Abotar Zaki Da dan Mutum Labari mai cike da al'ajabi
Abotar Zaki Da Mutum
Daga littafin LABARUN GARGAJIYA 2
Ibrahim Yaro Yahaya
Oxford University Press 1977
Ga ta nan ga ta nan ku.
Wani maharbi ne dai kullum yakan tafi daji yawon harbi ya harbo namun daji ya kawo gida. Matarsa ta wanke tukunya kafin ya zo. Idan ya zo sai ta karbi jakar da yakan kunso naman ciki, ta bude ta debi nama ta dafa.
To wata rana sai ya tafi daji yawon farauta. Ya yi ta yawo yana neman namun daji amma bai sami kome ba, har rana ta kusa faduwa. Har ya fid da rai, ya kama hanya zai tafi gida, sai ya ga fara, babe, ya kama ya kunshe ya dawo gida. Da isowarsa gida sai matarsa ta yi masa maraba, ta kawo masa ruwa ya sha.
Sai kuma ta dauko angararsa. Tana budewa ke nan sai fara ta tashi, fir! Sai ya ce, ‘Kash, abin da na samo ke nan tun safe. Bi ta ki kamo ta, in kuwa ba haka ba mu kwana da yunwa yau.’
Matar maharbin nan kuwa tana da tsohon ciki, ta kusa haihuwa. Sai ta bi faran nan a guje. Suna gudu, suna gudu cikin daji ba ta kama ta ba. Can tana cikin gudu sai ciwon haihuwa ya kama ta. Da ta ga ba za ta iya komawa ba sai ta shiga neman wani ke6a66en wuri a cikin dajin. Sai ta ga wata katuwar kuka mai kogo. Shi kuma kogon daga ciki ya rabu biyu. Bari daya wata zakanya ta haihu a ciki. Bari daya kuwa ba kowa a ciki. Sai ta shiga cikin kogon nan, kuma Allah ya ba ta sa ’a ta shiga barin da ba kowa cikinsa. Tana shiga sai ta haifi danta namiji.
Ana nan ana nan! sai ta dinga futa neman abinci tana barin jinjirin nan a cikin kogo. Idan ta sami abinci ta ci sai ta dawo cikin kogon nan inda ta boye dan nan nata ta ba shi nono ya sha.
Amma har yanzu matar nan ba ta san da zakanya a daya 6arin kogon ba, ita ma zakanyar ba ta san da zaman wannan matar ba.
Ana nan a kan haka sai wata rana zakanya ta fita ta tafi kiwo, ita ma wannan mata ta tafi neman abinci, sai ’ya’yansu, watau dan matar nan da dan zakanya suka fito bakin kogo shan iska, suka ga juna, Allah ya hada tsakaninsu suka yi abota. Duk lokacin da iyayensu suka tafi neman abinci sai su fito su yi wasa. Idan sun ga iyayensu sun kusa dawowa sai su koma cikin kogo abinsu. Shi kuwa dan zakanyar nan kullum sai ya yi wa dan matar nan kashedi cewa kada ya yarda uwarsa zakanya ta gan shi. In ta gan shi za ta kashe shi. Shi kuma yaro sai yakan ce, ‘to.’
Ana nan a haka har yara suka yi wayo. Dan zakanya ya kawo kafi. Sai zakanya ta ce masa, ‘To tun da yake ka kawo karfi, sai mu tafi da kai daji ka ga yadda muke bangazar namun daji.’
Suka fara tafiya daji tare da dan zakanya, don ya ga yadda zaki yake bankadar naman daji in yana so ya kashe shi ya samu abinci. Ran nan sai zakanyar ta fita ba tare da danta ba. Sai ta gamu da matar nan mai renon yaro a kogo, ta bangaje ta, ta fadi ta mutu, ta dauko ta kawo gida ta zube sharab a bakin kogo, ta ce wa danta, ‘Yau fa ga babban nama na samo maka.’
Dan zakanya ya gane cewa gawar matar nan ce uwar abokinsa ya ce, ‘Ni ba zan ci wannan naman ba. Na daina cin naman mutum, sai dai na gada, da fakara, da zabi, da bareyi, da jimina da sauransu.’
Sai uwar ta ci gaba da samo masa namun daji. In ta kawo masa sai ya diba ya gasa tsaf, ya kirawo abokin nan nasa su zauna su ci su koshi.
Ana nan ana nan ran nan sai zakanya ta tafi da danta daji don ta koya masa yadda ake bangazar nama sosai. Wancan zuwan da suka yi ba su ga namun daji ba ballantana ta koya masa. Suka tafi daji suka isa wani fili ta ce ya koma waje guda ya tsaya. Ya koma ya tsaya, ita kuma ta tafi nesa ta taho a guje buguzum buguzum ta kade shi a hankali. Ta ce da shi haka ake yi, amma idan naman daji za a kade da karfi ake dungurar sa. Ya ce ya gane. Ta sa shi ya gwada a kanta. Ya ja da baya ya doso ta da gudu ya yi kamar zai bangaje ta sai ya kuskure. Ta ce masa ba haka zai yi ba. Ta dada gwada masa.
Sau uku yana tahowa a guje buguzum buguzum kamar zai kade ta sai ya kauce. Ta yi fushi. Da ya ga ta fusata, da ma niyyarsa ya kashe ta don ya rama abin da ta yi wa uwar yaron nan abokinsa, sai ya taho da karfi ya kade ta ta fadi ta mutu.
Sai ya kirawo abokinsa ya zo, ya ga zakanya a mace, ya ce, “Yaya aka yi haka ?’
Dan zakanya ya ce, “Ni ne na kashe ta. Yanzu mun zama daidai. Ni da kai sai mu ci gaba da zaman duniya gaba daya. Allah zai taimake mu da abin da za mu ci mu sha.’
Yaro ya ce, ‘To.’
Suna nan tare abinsu har dan matan nan ya isa shayi. Sai dan zakanya ya ce masa, 'Ku mutane kuna da wata al’ada in za a yi muku kaciya. Tun da yake ka isa sha, sai ka tafi cikin gari ka nemi yadda ake yi. ’
Yaro ya tafi cikin gari ya isa gidan wata tsohuwa a kofar gari. Ya yi sallama.
Tsohuwa ta ce, ‘Samari daga ina?’ Ya ce, ‘Na yi batan kai ne. lyayena sun tafi sun bar ni ni kuma ban san kowa a garin nan ba.'
Tsohuwa ta ce, “To shi ke nan. Shiga cikin gida. Ka zama dana.‘ _
Ta ba shi daki. Suna nan tare har ta sa aka sha shi. Ya zauna a gidanta ya warke. Yana zuwa gun yara suna wasa har yara suka sa masa suna Dan Tsohuwa.
Ana nan haka har ya kawo gabar girma. Ya daina zuwa wasa wurin yara sai ya tafi ya tarar da abokinsa dan zakanya su yi hira da dare. ldan lokacin barci ya yi sai zaki ya rako shi har gida sa’an nan ya koma daji cikin kogonsa.
Suna nan a haka har Dan Tsohuwa ya isa aure. Zaki ya tambaye shi, ya ce, ‘Wace yarinya kake so duk garin nan? Zan yi maka dalili ka aure ta!
Yaro ya ce, 'Ni ba wadda nake so sai ‘yar sarkin garin.'
Zaki ya ce, ‘To zan yi maka hanya ka aure ta kuwa. Kuna zuwa wasa tare?’
Yaro ya ce, ‘I, muna zuwa. Kuma muna zuwa yin wanka a wani kogi tare da abokai da yawa.’
Zaki ya ce, ‘Za ka iya kwatanta mini ita 'yar sarkin ?'
Yaro ya ce, ‘Lokacin da za mu shiga wanka za ka gan ta ba ta shiga da wuri ba. Sai kowa ya gama shiga ita tana feleke tana yanga, har sai kawayenta sun ce da ita, ‘Mairam, ba za ki shigo wankan ba ne?’
Ita kuma sai ta ce za ta shiga ne. Sannan sai ta shiga.
Zaki ya ce, “To zan gane ta. Amma kamin ku je wurin wankan ni zan riga ku zuwa. In na je zan shiga ciki in buya. Sai kun je kuna cikin wanka, in ta shiga ruwa sai in yi sando in kama ta in fita waje in yi gurnani. Ka san kowa zai ji tsoro. Ku gudu gaba daya zuwa gari kuna cewa zaki ya kama Mairam.'
Dan Tsohuwa ya ce to ya ji.
Zaki ya tafi inda suke wanka ya shiga ya 6uya. Jim kadan sai ga su sun zo wanka. Kowa ya tu6e kayansa suka shiga wanka. Suna ta wanka amma Mairam ba ta shiga ba, tana ta kumi.
Sai kawayenta suka ce, ‘Mairam ba za ki yi wankan ba ne?’
Ta ce, ‘Ai zan shigo ne.’
Ta tu6e ta shiga wanka. Suna wanka suna wanka sai zaki ya lababo da sanda ya kama Mairam ya fito ya yi girgiza ya yi gurnani. Sai suka fita a guje zuwa gida. Da isarsu sai suka ce ai zaki ne ya kama Mairam a wurin wanka.
Sai sarki ya sa aka yi yekuwa kowa ya fito da shirinsa, fadawa da sarakunan baka na garin duk. Aka hadu, shirin yaki sosai. Aka yi hawa aka tafi bakin kogi. Aka ce, ‘Yaya za a yi a karbi Mairam a hannun zakin nan ?’
Wani daga cikinsu ya ce a harbi zakin. Wani kuma ya ce in an je garin harbinsa aka kuskure shi aka harbi Mairam fa? Aka dai kasa kar6o Mairam daga hannun zaki.
Sarki ya sa aka yi shela cewa duk wanda ya kar6o Mairam daga hannun zakin nan zai aura masa ita. Aka yi shela.
Kowa ya yi shiru. Aka rasa wanda zai fito ya kar60 ta daga hannun zakin nan.
Sai Dan Tsohuwa ya ce shi zai shiga ya karbo ta. Mutane sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan, suna mamaki suna cewa, ‘Ku ji yaro da kankanba. Duk su sarkin baka ma ba su ce za su iya ba, amma shi ya ce zai iya.’
Sarki ya ce, ‘Ku kyale shi tun da ya ce zai iya.’
Aka bar shi ya shiga. Ya doshi wurin zaki yana yi masa kirari, yana matsawa kusa da shi. Mutane suka yi shiru suna kallon sarautar Allah. Suna kallon yadda yaron nan zai kare da Zaki.
Dan Tsohuwa ya isa wurin Zaki. Zaki bai yi masa kome ba. Ya shafa gadon bayan Zaki, yana yi masa kirari. Har dai ya karbo Mairam daga wurin Zaki. Da karbar ta sai Zaki ya nutse cikin ruwa. Shi kuma ya fito da Mairam. Mutane kowa sai mamaki yake yi.
Aka dora Mairam da Dan Tsohuwa a kan dawaki aka taho ana kade-kade da bushe-bushe har aka iso gari. Da aka zo gida sai sarki ya daura musu aure. Aka tambayi inda Dan Tsohuwa yake so a gina masa gida. Ya ce ya fi so a gina masa a yamma da gari.
Aka kera masa gida. Ya sa aka yi kofa daga yamma saboda zakin nan abokinsa. Aka ke6e wani wuri dabam. Waje daya aka yi komi guda uku, daya a zuba nama, daya abinci, daya ruwa. Duk wannan an shirya ne don in zakin nan ya zo ya ci abinci ya sha ruwa.
Kullum kuwa sai Dan Tsohuwa ya sa a shirya abinci iri iri da soyayyen nama a zuba cikin komin nan. Shi kuma Zaki sai ya saci jiki ya zo gidan ya shiga ta kofar yamma ya ci abinsa. Ba wanda ya san abin da yake cinye abincin nan. Kuma ita Mairam ta bi diddigi, ta bi diddigi ba ta sami hakikanin abin da yake cinye abincin nan ba.
Ana nan a haka sai wata rana Sarki ya ce ya ba Dan Tsohuwa rabin kasarsa. Ya ce da shi ya shirya ya tafi ya ziyarci mutanen yankin da aka ba shi, don ya saba da su, su ma su saba da shi.
Dan Tsohuwa ya fada wa abokinsa zaki cewa zai yi tafiya ta kwana uku, amma za a ci gaba da ajiye masa abincinsa kamar yadda aka saba yi. Ya kuma gaya wa Mairam cewa a ci gaba da yin abinci ana ajiyewa a wurin nan. Ya kafa doka ya ce idan an zuba abinci, da zarar magariba ta yi kada kowa ya kusanci wurin da abincin nan yake ya yi sallama da mutanen gida ya tafi.
Fadawansa suka shirya suka yi hawa suka raka sabon sarki yawo cikin kasarsa. Aka bar Mairam da barori a gida.
Kullum Mairam tana shirya abinci barori na zubawa a wurin da aka saba. Kullum in sun zuba washegari sai su zo su tarar an cinye. Zaki yana zuwa da dare yana cinyewa. Ran kwana na uku, ranar da sarki zai dawo daga ziyarar kasarsa sai Mairam ta ce ita dai sai ta ga abin da yake cinye abincin nan.
Bayan an kai abinci sai ta sami wani wuri ta Iabe. Can kuwa sai ga Zaki ya taho cin abinci. Da ta gan shi sai ta kwalla ihu. Ta yi kururuwa. Ta ce, ‘Jama’a ku zo ga Zaki a gidan nan.’
Mutane suka cika gidan sabon sarki. Sai sarkin bakan garin ya fitar da kibiya ya harbe Zaki ya fita da gudu ya je bayan gari ya fadi ya mutu.
Sabon sarki ya doso gari. A kusa da garin ’yan tarye sai suka yi masa maraba. Wani daga cikinsu ya ce masa. ‘Ranka ya dade, Allah ya ja zamaninka. Ai jiya an auna arziki. Zaki ya shiga gidanka, sai Mairam ta gan shi ta yi kururuwa aka taru. Sai sarkin baka ya harbe shi ya gudu. Dafi ya debe shi a bayan gari ya fadi ya mutu. Ga shi can ma daga nan, har ya kumbura.‘
Sai sabon sarki ya tsinkayo abokinsa Zaki a kwance, a mace, duk ya kumbura. Sai suka tafi kan gawar. Da isowarsu sai sabon sarki ya kidime, bakin cikin mutuwar abokinsa ya kama shi. Sai ya zaro wuka ya soke kansa ya fadi ya mutu. Take a gurin sai ga gawar zaki da ta sabon sarki a jere.
To da can zaki ya kashe uwarsa zakanya saboda ta kashe uwar shi wannan sabon sarkin. Yanzu kuma shi sabon sarkin ya kashe kansa saboda ganin an kashe zaki abokinsa.
To a cikinsu wa ya fi alkawari?
Daga Bukar Mada
0 Comments: